ICC ta daure Katanga shekaru 12 a gidan yari | Labarai | DW | 23.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ICC ta daure Katanga shekaru 12 a gidan yari

Kotun da ke hukunta laifun yaki ta kasa da kasa ta ICC ta daure madugun 'yan tawayen Jamhuriyar Dimokradiyar Kongo Germain Simba Katanga tsawon shekaru 12 a gida yari.

Germain Katanga ICC Den Haag Urteil 23.05.2014

Germain Simba Katanga kenan a Kotun ICC yayin da ake yanke masa hukunci

Alkalin da ya jagoranci yanke wannan hukunci ya ce bisa shaidun da aka gabatar musu Katanga na da hannu dumu-dumu a wani kisan kiyashi da mayakan sa kai na lardin Ituri suka yi a kauyen Bogoro da ke gabashin Jamhuriyar Dimokradiyar Kongo a shekarar ta 2003.

To sai dai kotun ta wanke Katanga din daga zarge-zargen da aka yi masa na fyade da yin amfani da kananan yara a matsayin mayaka yayin da a hannu guda alkalin kotun ya ce za a rage shekaru 7 daga 12 da aka yanke masa tunda ya rigaya ya share tsawon shekaru bakwai a tsare.

Guda daga cikin lauyoyin da suka kare Katangan yayin shari'ar ya shaidawa kamfanin dillancin labari na AFP cewa za su yi nazarin hukuncin da kotun ta yanke kafin su kai ga tsaida shawara ta daukaka kara ko akasin haka.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman