ICC: Gurfanar da jagororin Anti-Balaka | Labarai | DW | 13.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ICC: Gurfanar da jagororin Anti-Balaka

Mahukuntan kasar Faransa sun bayyana cewa za su mika jagoran 'yan tawayen nan na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Patrice-Edouard Ngaissona zuwa kotun kasa da kasa mai hukunta manyan laifuka ta ICC da ke birnin The Hague.

Ana dai zargin Patrice-Edouard Ngaissona da laifukan yaki a kasarsa ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Masu gabatar da kara dai sun bayyana cewa Edouard Ngaissona shi ne jagora a kungiyar sa kai ta Anti-Balaka wacce ke kai hare-hare kan Musulmi musamman a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2014.

A farkon wannan shekarar ne dai aka zabi Ngaissona cikin jagororin kwamitin hukumar da ke shirya wasannin kasashen Afirka ta CAF duk kuwa da shan suka daga bangaren kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch. Tuni dai aka cafke Alfred Yekatom da shi ma ake zargi da laifukan yakin a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wanda aka mika shi zuwa kotun ta ICC a watan da ya gabata.