Ibrahim Boubacar Keita ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na Mali | Siyasa | DW | 13.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ibrahim Boubacar Keita ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na Mali

Tuni abokin takarasa Soumaila Cisse ya amince ya sha kaye a zaɓen da zai sake mayar da ƙasar bisa turba ta Demokraɗiyya.

Matakin na Soumaila Cisse tsohon ministan kuɗin ƙasar ɗan shekaru 63 a duniya ya ba da mamaki dangane da tattaki da ya yi , da shi da iyalensa zuwa gidan sabon shugaban ƙasar inda ya yi masa barka tare da fatan alheri a game da sabon nauyin da 'yan ƙasar Mali suka dora masa tun kafin ma a bayyana sakamakon zaɓen a hukumance.

Jama'a na yin marhabin da matakin Cisse na zuwa gidan sabon shugaban don yi masa barka

Titel: DW_Soumaila-Cisse1 und 2 Schlagworte: Bamako, Präsidentschaftswahl, Spitzenkandidat, Staatsstreich, Soumaïla Cissé, URD (Union pour la République et la Démocratie, Union für Republik und Demokratie) Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Katrin Gänsler Wann wurde das Bild gemacht?: 29. Juli 2013 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Bamako, Mali

Soumaila Cisse

Bai dai kasance wata al'ada ba a ƙasar ta Mali wanda ya sha kaye a zaɓe ya yi irin wannan tattaki ba domin yin barka,inda wayar tarho kawai ta isa kamar yadda a ke yi a wasu ƙasashe, tuni kuma wannan mataki ya buɗe wani sabon babi ga rayuwar Soumaila Cisse a ƙasar ta Mali dama wajenta, kamar yadda wannan mutumin ya bayyana :

Ya ce : ''Wannan matakin na Soumaila Cisse abin yabawa ne, ya kuma nuna cewa,ya na kishin demokraɗiyya kuma dukkanin 'yan ƙasar Mali na yin marhabin da haka.''

Shugabannin duniya na yi masa murna da samun nasarar

French President Francois Hollande arrives for the European Council meeting at the EU headquarters in Brussels on June 27, 2013. European Commission President Jose Manuel Barroso on Thursday announced a political deal on the EU's hotly contested 2014-2020 trillion-euro budget, hours before an EU summit mulls how to get millions of jobless youths back into the workplace. AFP PHOTO / GEORGES GOBET (Photo credit should read GEORGES GOBET/AFP/Getty Images)

Francois Hollande ya aike da sakon tayya murna ga IBK

Shugaban ƙasar Faransa Francois Hollande ya isar da sakon barkarsa zuwa ga sabon shugaban Ibrahim Boubacar Keita tare kuma da yin alƙawarin halartar bikin rantsar da shi da za a gudanarwa a watan Satumba mai zuwa.

Babban ƙalubalen da ke a gaban sabon shugaban ƙasar shi ne ɗaukar matakan gaggauwa da za su kawo yarda da juna tsakanin 'yan ƙasar da ke fama da rarrabuwar kawuna tun bayan ɓullowar rikicin shekarar 2012, wanda ya bai wa 'yan tawaye da ƙungiyoyin kishin islama damar mamaye yankin arewacin ƙasar,bayan juyin mulki ranar 22 ga watan Maris na shekarar 2012 wanda sojoji suka yi.

A lokacin da yake ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa IBK ya ce abin da zai fara mayar da hankali a kansa idan ya samu nasara a zaɓen shi ne sasanta 'yan ƙasar , to ko ya ya ƙungiyar 'yan tawayen MNLA ta karɓi wannan labari na nasarar ta IBK Ag Assarig shi ne kakakin ƙungiyar:

Ya ce ''Muna jira ganin sabon shugaban ya buɗe tattaunawa tsakaninmu, tattaunawar da muke buƙatar a shirya a kan turbar ta gaskiya da daidaito.''

A yanzu dai abin da ya ragewa sabon shugaban ƙasar bayan an rantsar da shi, dage damtse don tinkarar matsalolin da ke addabar ƙasar waɗanda suka haɗa da rashin tsaro da talauci da kuma rashi aikin yi na matasa.

Daga ƙasa za a iya sauraran wannan rahoto

Mallawafi : Yusuf Abdoulaye
Edita : Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin