1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hunkuncin daurin rai da rai ga 'yan awaren Maroko

Umar Saleh SalehFebruary 18, 2013

Wata kotun sojin a Maroko ta yanke hunkuncin rai da rai ga wasu 'yan aware na yankin Saharawi, bayan da aka same su da laifin kisa ga dakarun kasar.

https://p.dw.com/p/17fuZ
Hoto: Karlos Zurutuza

Wata kotun sojin kasar Maroko, ta yanke wa wasu mutane 24 hukunci mai tsanani, bayan da ta same su da laifin kisan wasu dakarun kasar a shekara ta 2010.
Kotun dai ta caji mutanen su 24 'yan asalin yankin Saharawi da laifin halaka sojojin kasar 13 tare da raunata wasu da dama a lokacin da suka kutsa a yankin na Saharawi, yankin da ke neman ballewa daga kasar ta Maroko.
Kungiyoyin kare hakin bil adama sun nuna damuwarsu ga abunda suka kira hukunci mafi tsanani, kana an yi shi ba cikin adalci ba.
Mutane 22 ne dai daga cikin 24 suka fuskanci hukuncin daurin rai da rai yayin da aka yanke wa mutum biyu hukuncin daurin shekaru 30 a gidan wakafi.
A shekara ta 1975 ne kasar Maroko ta mamaye yankin da ta maida har ya zuwa yau a matsayin wani sashen kasarta, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta kira bangarorin biyu da su kai zuciya nesa domin kawar da zubar da jini a yakin da ya barke tsakanin bangarorin biyu, abunda kuma yayi sanadiyar mutuwar dubban mutane daga kowane bangare.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mohammad Nasiru Awal