1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hungary Za a hukunta masu tallafa 'yan cirani

Zulaiha Abubakar
May 29, 2018

Firaministan kasar Hungary Viktor Orban ya mikawa majalisar dokokin kasar wata doka a kan masu taimakawa 'yan cirani har su samu shaidar cigaba da zama a kasar.

https://p.dw.com/p/2yYna
Viktor Orbán
Viktor OrbánHoto: imago/Panoramic International/C. Licoppe

Dokar dai na a sahun gaba cikin kudirorin firaiministan kasar kan bakin haure. Ko da yake hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta shawarci kasar ta Hungary da ta yi watsi da batun nan na takaita ayyukan kungiyoyi masu zaman kansu a fadin kasar sakamokon rashin yin hakan zai iya janyo guguwar nuna kyama a fadin kasar.