Huldar tattalin arzikin Najeriya da China | Siyasa | DW | 07.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Huldar tattalin arzikin Najeriya da China

A kokarin tabbatar da sabon matsayinta na kan gaba a cikin nahiyar Afirka ta fannin tattalin arziki Tarayyar Najeriya ta rattaba hannu bisa wasu yarjejeniyoyi har guda 17 da China

Daya dai na zaman mafi girma ga batun tattalin arziki a nahiyar Afirka, amma a takarda, dayan kuma ta kama hanyar fintinkau wa duniya ga manyan kasashen, Tarayyar Najeriya da na China da shugabanninsu suka zauna suka rattaba hannu kan jeri na yarjejeniyoyin, da nufin tabbatar da ci-gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umarsu.

Kama daga yaki da ta'addancin da China tace tana shirin sa hannu da nufin tabbatar da kaiwa karshe, ya zuwa gina wani layin dogo na zamani a gefen tekun kasar dama inganta harkokin sufurin sama, dama batun hasken wutar lantarki da harkar noma, kasashen biyu dai sun ce tana shirin yin karfi a sabuwar dangantakar.

Mutum na biyu mafi karfin ikon China kuma Firimiyan kasar Li Keqiang da ke wata ziyarar aikin farko zuwa a Abuja dai ya fadawa mai masaukin nasa fa cewar China shiriye take domin cimma wannan burin.

“Ina da imanin kasashen mu biyu na bukatar musanya mai matukar tasiri a tsakanin al'ummar mu, da karfafa tattaunawa mai ma'ana, da kuma ci-gaba da taimako da goya bayan juna kan batutuwan da muke da tunani iri guda kansu. Kuma muna bukatar aiki tare da nufin tabbatar da yaki da ta'addanci”

Keqiang dai na zaman jami'in wata babbar kasa ta duniya dake isa Abuja, kuma zai taka rawa cikin taron tattalin arziki na duniyar da birnin na Abuja ke dauka. Abun kuma da ake yi wa kallon alamu na karin tasirin China a Najeriyar, dama nahiyar da a cewar firimiyan, ciniki a tsakanin juna na shirin zuwa dallar Amurka milliyan dubu 400 nan da wasu shekaru shida masu zuwa.

A bara kadai dai Najeriya da ke mai masaukin Keqiang din dai, ta yi harkar da ta kai dallar Amirka milliyan dubu 13 a tsakaninta da sinawan da sannu a hankali, ke mamaye harka ta kasuwanci a kasar. Abun kuma da a fadar Ministan harkokin wajen kasar Aminu Bashir Wali ke da ruwa da tsaki da sabuwar guguwar sauyin da ke kadawa a kasar ta Najeriya yanzu haka.

“Baya da China din nan matsayinsu kusan dai dai yake da namu a wajen kasashen turai, yau in ka tuna ban dade da dawo daga China a matsayin jakadar Najeriya a Sin. In aka lura da abubuwan dake faruwa a can za'a ga su kansu manyan kasashen turai suna kan hanya domin neman taimakon gwamnatin China, saboda haka ina.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin