Huldar Jamus da Rasha na nan daram | Labarai | DW | 10.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Huldar Jamus da Rasha na nan daram

A lokacin da Angela Merkel ta gana da mai masaukin bakinta shugaba Vladimir Putin na kasar ta Rasha abirnin Mosko, shugabar ta gwamnatin Jamus ta kara jaddada mahimmancin hadin kan kasashen biyu.

Russland Angela Merkel & Wladimir Putin

Shugaba Merkel da shugaba Putin

A ziyarar ba zata da ta kai kasar Rasha ranar Lahadinan, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta ziyarci kabarin dogon yaro na sojojin Tarayyar Soviet da suka kwanta dama, lokacin yakin duniya na biyu, inda ta bukaci a samar da hadin kai da Rasha bayan shiga yanayi na tankiya saboda rikicin kasar Ukraine.

Shugaba Merkel ta je birnin na Mosko ne inda ta ajiye furanni a kaburburan sojojin, wadanda da suka mutu a lokacin yakin a matsayin karramawa, bayan da ta tsallake halartar gagarumin bikin faretin soji da kasar ta Rasha ta tsara a ranar Asabar.

A lokacin da ta gana da mai masaukin bakinta shugaba Vladimir Putin na kasar ta Rasha, Merkel ta kara jaddada muhimmanci da hadin kai ke da shi.

Ta ce ya zama dole su yi aiki tare su hada kai ciki kuwa har da batutuwa masu sarkakiya.

Cikin batutuwan da shugabannin suka tattauna, ya hada da rikicin Ukraine wanda shi ke kan gaba, inda shugaba Merkel ta ce ya zama dole a samar da zaman lafiya a kasar a siyasance.