Huldar diplomasiyya tsakanin Kyuba da Amirka | Labarai | DW | 19.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Huldar diplomasiyya tsakanin Kyuba da Amirka

Za a sake buɗe ofisoshin jakadanci tsakanin Amirka da Kyuba, bayan katseta da aka yi tun a shekarun 1961, saboda rashin zutuwar da aka samu tsakanin ƙasashen biyu.

Nan gaba a daran yau Lahadi zuwa gobe Lititin aka shirya Amirka da Kuyba za su sake buɗe ofisoshin jakadancinsu a birnin Havana da Washington.

Wannan al'amari dai na zaman wani mataki na farko na sake farfaɗo da hulɗa diplomasiyya tsakannin ƙasashen biyu,bayan ganawar tarihi da aka yi a bara tsakanin shugaban Amirka Barack Obama da Raul Castro a Havana.

Hulɗar diplomasiyya tsakanin ƙasashen biyu ta tsinke tun a shekaru 1961 lokacin da Amirka ta ƙaƙabawa Kyuba takunkumin karya tattalin arziki saboda manufinta na siyasa waɗanda ta kamanta da na 'yan ta'adda.