Hulda tsakanin Tarayyar Turai da kasar Kyuba | Labarai | DW | 06.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hulda tsakanin Tarayyar Turai da kasar Kyuba

Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar cewa babu wata gasa tsakaninta da Amirka wajen neman kulla kyaukyawar hulda da kasar Kyuba.

Tarayyar Turai ta kara da cewa, farfado da dangantaka tsakanin kasar ta Kyuba da Amirka, na iya taimaka wa masu hulda da kasar ta Kyuba a fannoni da dama, kuma ta ce babu batun gasa ko neman shiga gaba, amma kawai ta neman kara karfin hulda ce da kasar ta Kyuuba.

Wadannan kalammai dai sun fito ne daga jagoran tattaunawa na Tarayyar Turai Christian Leffler, yayin da yake magana da manema labarai a birnin Havana babban birnin kasar ta Kyuba, inda ya halarci wani zama na uku na tattaunawarsu da kasar ta Kyuba wanda suka soma yau da watanni 11 da suka gabata, a wani mataki na neman farfado da hulda tsakanin Kyuba da Tarayyar Turai da ta tabarbare tun a shekara ta 2003.