Hulɗar cinikayya tsakanin Nigeria da ƙasar Sin | Labarai | DW | 27.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hulɗar cinikayya tsakanin Nigeria da ƙasar Sin

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta amince da baiwa ƙasar China lasisin wasu rijiyoyin mai guda huɗu, yayin da ita kuma China, za ta zuba jari na kimanin Dala biliyan hudu a ƙasar ta Nigeria. Yarjejeniyar wadda shugaban Nigeria Olusegun Obsanjo tare da takwaran sa na ƙasar Sin Hu jin-tao dake ziyarar rangadi a Nigeriar suka sanyawa hannu, ita ce mafi girma daga cikin yarjeniyoyi bakwai da suka kulla domin bunƙasa hulɗar cinikayya dana tattalin arziki a tsakanin ƙasashen biyu. Bugu da ƙari, ƙasar ta China ta yi alƙawarin taimakawa Nigeria wajen yaƙi da cutar Malaria dana zazzabin murar tsuntsaye. Yarjejeniyar ta kuma haɗa da gyaran matatar mai ta Kaduna da kafa tashar samar da hasken wutar lantarki. A jawabin sa shugaban ƙasar China Hu Jin-tao ya baiyana cewa maƙasudin ziyarar sa a Nigeria ita ce, ƙarfafa dangantakar da ta daɗe a tsakanin ƙasashen na su. A yau ne dai shugaban kasar ta China zai yiwa zaman haɗaka ta majalisun dokokin Nigeriar jawabi kafin daga bisani ya wuce zuwa ƙasar Kenya.