Hulɗa tsaro tsakanin Amirka da Masar | Siyasa | DW | 07.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hulɗa tsaro tsakanin Amirka da Masar

Yayin da Ƙungiyar Tarrayar Turai ta dakatar da ba da tallafin tsaro ga Masar, Amirka na ci gaba da bai wa ƙasar tallafi .To amma shugaba Barack Obama ya ce za su sake nazari.

Amirka na ware ko wacce shekara biliyan ɗaya da rabi ga ƙasar ta Masar domin tallafa wa harkokin soji da tsaro,kuma duk da ma sojojin sun kifar da zaɓaɓiyar gwamnatin Muhammed Mursi, amma har yanzu Amirka ba ta daina ba da tallafin ba saboda yadda ta ke kallon za ta rasa wani sukunmi na hannu a sha'anin tsaro a yanki da ke da mahimmanci a gareta.

Tushin yarjejeniyar ba da tallafin ga Masar da aka cimma

U.S. President Barack Obama arrives to deliver remarks on the government funding impasse at M. Luis Construction, a local small business in Rockville, Maryland, near Washington, October 3, 2013. Obama travelled to the business to highlight the impacts that a government shutdown and default would have on the economy. Obama blamed congressional Republicans for the government shutdown on Thursday, saying the budget stalemate is caused by their obsession with hobbling his healthcare plan and the sway of Tea Party-backed conservatives over party leaders. REUTERS/Jason Reed (UNITED STATES - Tags: POLITICS BUSINESS HEALTH)

Shugaba Barack Obama

Ba da tallafin na soji ga ƙasar ya samo asili ne tun yarjejeniyar da Amirka ta ƙula da Masar ɗin a shekarun 1979.Kuma Masar ta kasance ƙasar da ke cike da mahimmanci ga Amirkar ba ma dan saboda mashigin teku ba na Canal de Suez , shi kansa batun tabbatar da tsaron Isra'ila na zaman wani abin da Amirkan ke karewa. To amma a yanzu shugaba Barack Obama ya ce za su saka ido a kan wannan batu.Ya ce : '' Abin da muke yi a yanzu na hulɗa tsakanin mu da Masar wani abu ne da ke tassar mana da tsada, amma babu shakku a kan wannan matsayi da aka cimma za mu duba abin da ya fi zama riba da alheri ga al'ummar Masar da kuma Amirka.''

Nazari na masu yin sharhi a kan wannan batu mai mahimmanci

Egypt's Armed Forces General Abdel Fattah al-Sisi (R) meets with U.S. Senators' John McCain (C) and Lindsey Graham at the Ministry of Defense in Cairo in this August 6, 2013 handout picture provided by the Ministry of Defense. Republican senators Graham and McCain arrived in Cairo at President Barack Obama's request to meet with members of the new government and the opposition. The Muslim Brotherhood on Monday rejected pleas from international envoys to swallow the reality that Mohamed Mursi will not return as Egypt's president. The envoys from the United States and the European Union, trying to resolve a political crisis brought on by the army's overthrow of the Islamist Mursi a month ago, visited jailed Brotherhood deputy leader Khairat El-Shater in the early hours of Monday. REUTERS/Ministry of Defense/Handout via Reuters (EGYPT - Tags: POLITICS MILITARY) ATTENTION EDITORS - THIS IMAGE WAS PROVIDED BY A THIRD PARTY. FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. NO SALES. NO ARCHIVES. THIS PICTURE IS DISTRIBUTED EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS

Janar Abdel Fattah al-Sisi tare da John McCain

Majalisun dokokin Amirka sun daɗe suna shakku a kan wannan shiri na tallafa wa sojojin, wanda da zaran sun amince da dokar ake isar da kuɗaɗen a cikin bankunan ga kamfanonin ƙera makamai da kayan yaƙi na soji wanda aka bai wa kamfanonin Amirka kwangilar ayyukan. Kuma kuɗaɗen da aka ware ba su fita daga Amirka domin abin kan kasance tuwo na mai na. Shana Marshall wata mai binciken kimiyya ce da ke a jami'ar George Washington wanda ta ce a kwai lauje cikin naɗi cikin wannan tallafi. Ta ce :''Lokaci zuwa lokaci a duk sanda maganar wannan tallafi ta zo a gaban 'yan majalisun dokoki, a kwai wasu manyan kamfanonin masu ƙera kayan yaƙi da tsaro, da ke tura mutanensu wajen 'yan majalisun dokokin domin yin kamun kafa. Cewar a kwai buƙatar a ci gaba da ba da tallafin sojin ga Masar saboda tsayawar shirin zai iya janyo rashin aikin yi ga wasu Amirkawan da kuma asara ga kamfanoni.''

Ba da tallafin ya dogara ga sauyi na demokradiyya da za a samu a Masar

US Secretary of State Kerry holds a press conference at Foreign Ministry concerning the intervention of Egyptian security forces in Cairo, Egypt. Bariskan Unal - Anadolu Agency

Sakataran harkokin wajen Amirka John Kerry

Tun can da farko Obama ya yi gargaɗin cewar cire tallafin Amirka ga Masar ɗin ba zai dakatar da yunƙurin sojin da suka kifar da gwamnatin Mursi ba. Sannan kuma ba zai iya kawo wani sauyi ba, to amma dai ana ganin halin da ake ciki a ƙasar ya sa Amirkar cikin tsaka mai wuya inji Shana. Ta ce: '' Watakila waɗannan kuɗaɗen tallafi da ake bai wa Masar za a jirgitasu zuwa wasu ƙasashe inda Amirka ta ke da yarjeniya da su ta tsaro, irinsu Iraki da Afganistan da Pakistan da kuma Somaliya. Kuma kamfanonin Amirka da ke cin wannan gajiya shekara da shekaru na iya sake samin wannan kwangilar.

Daga ƙasa za a iya sararon wannan rahoto da kuma wanda wakilinmu na Masar ya aiko mana dangane da halin da ake ciki a Masar.

Mawallafi : Delcker Janosch/Hassane
Edita : Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin