1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukunta masu cin hanci a Kamaru

January 14, 2015

Tsohon ministan kudi da tattalin arziki a kasar Kamaru Polycarpe Abah Abah, zai fuskanci zama a gidan kaso har na tsawon shekaru 25 saboda badakalar cin hanci da rashawa.

https://p.dw.com/p/1EKd5
Kamerun Präsident Paul Biya
Shugaba Paul Biya na KamaruHoto: imago/Xinhua Afrika

Wata kotu ta musamman da ke bincikar masu wawaso da babakere da dukiyoyin al'umma ta sami Abah Abah da laifin kwashe CFA miliyan dubu shida kwatankwacin miliyan goma sha daya na dalar Amirka da yayi amfani da su wajen siyan motoci da gidaje na kawa.

Kotun za ta kwace gine-gine 30 da motocin hawa takwas da taraktocin noma uku, sannan ta kwace asusun bankinsa da ke da kudi CFA miliyan 26 dukkansu mallakin na Abah Abah, wanda aka gurfanar da shi tare da wasu mutanen uku da suka hada har da Pascal Manga da aka saurari shari'arsa duk da cewa baya nan kamar yadda shedu suka tabbatar.

Abah Abah ya rike mukamin minista daga shekarar 2004 zuwa 2008, kafin nan ya rike sashin kula da haraji a ma'aktar kudi ta kasar. Ya kuma bayyana wannan hukunci da aka yi masa a matsayin "wasa" da ya ce zai daukaka kara.

Shi dai tsohon ministan Abah Abah ya zo hannu ne a shekarar 2008, karkashin wani shiri na yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Shugaba Paul Biya ta kaddamar a shekarar 2006 mai suna Sparrowhawk a turance.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Mohammad Nasiru Awal