Hukuncin yan Tarzoma a Britania | Labarai | DW | 30.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukuncin yan Tarzoma a Britania

An samu wasu yan britania guda biyar da laifin shirin kai hare hare a sassan kasar ta hanyar amfani da boma bomai da akayi da takin zamani.wata kotu dake birnin London ta saurari yadda wadanda ake zargin sukayi bayanan shirya boma boman ,da kuma inda zasu kai hare haren ,wadanda suka hadar da wuraren rawa na shakatawa, da cibiyoyin ciniki da kuma cikin jiragen kasa,wadanda ke nufin inda akwai cunkoson jamaa.Lauya mai mai gabatar da kara a madadin gwamnatin Britania,ya bayyana cewa wadannan mutanen biyar sunyi niyyan daukar fansa ne akan Britaniya ,sakamakon goyon bayanta wa Amurka a yaki da ayyukan tarzoma ,tun bayan harin 11 ga watan Satunba 2001.An dai dauki tsawon shekara guda ana sauraron shariar wadannan mutane biyar,wadanda kuma akace suna alaka da haren haren tashoshin jiragen kasa da aka kai a watan yuli 2005, a birnin London.