Hukuncin ta′addanci na farko a Jamus | Siyasa | DW | 12.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hukuncin ta'addanci na farko a Jamus

A karo na farko wata kotu a Munich ta yanke hukuncin daurin shekaru bakwai akan wani dan Iraki bisa laifin ta'addanci

Shi dai Muhammed Lokman, mai kasumba, bai nuna wata kaduwa ko ta miskala-zarratin a game da hukuncin da aka yanke masa ba. A lokacin da yake magana da yawunsa lauyan Muhammed Lokman ya ce fursunan ya musunta ikirarin da ake yi na cewar shi dan wata kungiya ce ta ‘yan ta’adda mai suna Ansaral-Islam dake gudanar da ayyukanta a kasar Iraki. Amma ita kotun da ta ci shari’ar a birnin Munich ta dage akan cewar fursunan dake da shekaru 31 da haifuwa, ko shakka babu, dan kungiyar Ansaral-Islam ne, wadda kungiya ce ta ‘yan ta’adda, kamar yadda aka ji daga bakin alkalin kotun Bernd von Heintschel-Heinegg. Alkalin ya ce kungiyar tare da reshenta na Jaisch-Ansaral-Sunna sun gwagwarmayar kafa wata janhuriya ce ta Islama a kasar Iraki. Kuma wadannan kungiyoyi guda biyu suke da alhakin hare-hare masu yawa, abin da ya hada har da farmakin da aka kai kan shelkwatar kwamitin red cross dake birnin Bagadaza. Alkaluma sun nuna cewar wadannan ‘yan ta’adda sune ke da alhakin hare-hare 280, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu daya a wajejen karshen shekara ta 2004. Ana zargin Muhammed Lokman da laifin taimaka wa kungiyar Ansaral-Islam da kudi da kuma kayan aiki daga mazauninsa a birnin Munich a cewar kotun a cikin dalilan da ta bayar game da hukuncin da ta yanke masa. Da wannan hukunci na daurin shekaru bakwai kotun ta amsa rokon da mai daukaka kara da sunan gwamnati Ulrich Bötha, wanda yake cewar:

Bin diddigin laifukan da ake zarginsa da aikatawa bai kasance mai sauki ba, saboda an gudanar da wannan aiki ne a ketare. Wani gagarumin aiki ne aka gabatar, inda aka tara na shaida masu yawan gaske.

Amma ita kanta kotun ta fito fili ta hakikance da gaskiyar cewar ba za a iya tantance halin da ake ciki a Iraki daga nan Jamus ba. Sai dai kuma Muhammed Lokman yana taka muhimmiyar rawa a tsakanin ‘ya’yan kungiyar ta Ansaral-Islam dake nan Jamus saboda shi ne mai sadarwa tsakanin shuagabannin kungiyar a Iraki da ‘ya’yanta dake kasashen yammacin Turai. Kazalika shi ne ke tara wa kungiyar kudi da kuma daukar dakarunta na sa kai, wandanda akalla daya daga cikinsu yayi asarar ransa a wani mataki na harin kunar bakin wake. Tuni dai lauyarsa mai suna Nicole Hinz ta ce zata sake daukaka kara domin sake bitar wannan hukunci, ko da yake ta ce ita da fursunan ba su yi mamakin hukuncin ba.

Tun da farkon fari ya bayyana shirinsa na rungumar hukuncin. Yana sane da abin dake tafe kuma maganar yawan shekarun da aka yanke masa Ya-Alla shekaru shida ne da rabi ko shekaru bakwai, bata taka wata muhimmiyar rawa a halin da ake ciki yanzun.