Hukuncin rikicin Nijar da Burkina Faso | Labarai | DW | 16.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukuncin rikicin Nijar da Burkina Faso

Lokacin da ta yanke hukunci a Hague, kotun duniya ta mayar da wani yanki na kudancin Nijar zuwa kasar Burkina faso, yayin da ta fadada arewacin kasar ta Nijar.

Kotun kasa da kasa ta yanke hukunci game da rikicin kan iyaka da ke tsakanin Jamhuriyar Nijar da makwabciyarta Burkina Faso, inda ta bayyana wani bangaren na Burkina Faso a matsayin yanki na arewacin Nijar yayin da wani yankin na kudancin kasar ta Nijar ya koma kasar Burkina faso. Wannan hukuncin ya shafi kilometa 380 na iyakokin da kasashen biyu suka gada a shekarar 1960 daga turawan mulkin mallaka na Faransa.

Dukkanin bangarrorin biyu da abin ya shafa sun nuna gamsuwa game da hukunci da aka yanke a kotun Hague da ke kasar Holland. Ministan shari'a na Nijar Morou Amadou wanda ya halarci zaman kotun, ya nunar da cewa kasarsa za ta ci gaba da ma'amala da makwobciyarta Burkina faso. Yayin da shi kuma ministan cikin gidan Burkina faso Jérôme Bougouma ya bayyana cewa daga yanzu rikicin ya zama tarihi.

Jamhuriyar Nijar da Burkina faso sun shafe shekaru suna takkadama akan wasu sassa na kan iyakokinsu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar