1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin Kisan El-Sherbini

November 11, 2009

Kotun birnin Dresden dake gabashin Jamus ta yanke hukuncin ɗaurin rai da rai ga Bajamushen nan da ya kashe wata 'yar ƙasar Masar mai suna Marwa El- Shribini.

https://p.dw.com/p/KU98
Marwa El-SherbiniHoto: AP

Tun dai lokacin da shi Alex Wiens da zai cika shekaru 29 alhamis ya ƙi nuna alamar nadama da aikata kisan gillar da a ke zargansa da shi, aka san cewa ta faru ta ƙare wa Bajamushen ɗan asalin ƙasar Rasha. Dalili kuwa shi ne, bisa wannan ƙwaƙƙwarar hujjar ce, kotun ta birnin Dresden ta dogara wajen aiwatar da hukunci mafi tsanani da dokokin Jamus suka tanadar, wato ɗaurin rai da rai.

Dama kuma lauya da ke kare marigayi Marwa El-Sherbini ya gabatar da fannonin doka da ke nuna cewa kisan gillar da aka yi wa ita 'yar ƙasar ta Masar mai shekaru 31 da haihauwa, ba a bukatar shaidu tun da a gaban ɗimbin mutane da suka hallara a kotun ya aikata. Yana mai cewa kisan ma kintsattsiya ce, domin akwai cikakkun bayannai dake nuna cewar tun da farko aka shirya wannan kisan kai, musamman ganin yadda aka riƙa sukan wannan matar da wuƙa ba ƙaƙƙautawa. Sa´annan kuma an aikata wannan ɗanyen aikin ne a gaban idon ɗanta mai shekaru uku kacal da haihuwa. Ko shi ma Wolfgang Donsbach, malamin hulɗa da jama´a a jami´ar fasaha ta Dresden yayi tsokaci ya na mai cewa:

"Idan aka yi la´akari da abubuwan da suka gabata, to ina ganin cewa da gangan ya aikata wannan kisan. Ya so ya haifar da wani yanayi da zai karkatar da hankulan mutane, saboda haka ne ma wasu suka dinga ganin kamar dai da matsin lambar siyasa. Amma kuma alƙali ta yi aikinta yadda ya kamata".

Ita dai alkali Brigit Wiegand da ta yanke wannan hukunci ta bayyana cewa shi Alex Wiens da ya shigo Jamus daga Rasha a lokacin da ya fara wayo, ya fara ƙyamar jinsi ne bayan da ya rasa aikinsa. Amma dai ba za a iya sauraran ƙarar da ya ke da niyyar ɗaukakawa a kowace kotu ce ta Tarayyar Jamus matuƙar bai shafe shekaru 15 cur a gidan waƙafi ba.

Shi dai Alex Wiens ya kai wa marigayiyar hari ne a cikin kotu a ranar ɗaya ga watan yuli, yayin da ake sauronsu kan shigar da ƙara da ita Marwa El-Shribini tayi sakamakon zazzaginta da yayi ta yi a bainar jama'a, yana mai nuna ƙyamarsa a gareta a matsayinta na musulma mai sanya hijabi, inda yayi ta daɓa mata wuƙa a kotun har so goma sha shidda tare kuma da yin barazanar kashe mijinta da yazo domin ceton ta. A saboda haka ne ma Werner Wendel na hukumar da ke kula da harkokin baƙi na Dresden ya ce wadi na tsaka mai wuya sun taimaka ma Alex rungumar manufofin Nazi, inda ya ce:

"Bai yi nasarar sajewa da tsarin rayuwa irin na Jamus ba. Bai yi sa´ar samun madogara da zata ba shi damar zama ɗan ƙasa na gari ba. Ba kintsattsen mutum ba ne, amma kuma za a iya danganta shi da tsageran da suka kasa sajewa da rayuwa ta Jamus".

Wasu daga cikin mazauna Alƙahira da ke zama babban birnin ƙasar da a ka haifi ita Marwa sun bayyana gamsuwarsu da wannan hukunci da a ka yanke ma wanda ya kashe ta saboda dacewa da yayi da manufofin ƙasar ta Jamus da a ka aikata ɗanyar a cikinta. Sai dai wasu na ganin cewa ba hukuncin da ya kamata a aiwatar ma shi Alex Wiens illa hukunci kisa. Shi kuwa jakadan Masar a Jamus, Ramzy Ezzeddin Ramzy cewa yayi, idan a ka danganta ɗaukacin Jamusawa da ƙyamar jinsi, to lalai ba a yi musu adalci ba. Ya kuma ƙara da cewa:

"Mutane ne da suka san ya kamata. Amma ba dukkaninsu ke marhabin da baƙi da hannun bi-biyu ba. Waɗanda ke irin wannan hali na ƙyamar jinsi ba su da yawa a cikinsu ".

Kimanin Jamusawa musulmi da suka kai 100 ne dai suka yi maci a wajen kotun na Dresden domin yin Allah Wadarai da amfani da a ke yi da manufofin ƙyamar baƙi da a ke watsawa ta kafofin internet wajen nuna ƙyamar jinsi a ƙasar.

Mawallafi: Mouhammadou Awal Balarabe

Edita: Ahmad Tijani Lawal