1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin kisa ya ragu a duniya

Yusuf Bala Nayaya
April 12, 2018

Kasashe da ke kudu da hamadar Saharar Afirka sun yi rawar gani a kokari na rage yawaitar aiwatar da hukuncin kisa a cewar rahoton kungiyar Amnesty International.

https://p.dw.com/p/2vu6U
Japan Welttag gegen die Todesstrafe
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Tsuno

Kungiyar Amnesty International ta fitar da rahotonta na shekara-shekara a wannan rana ta Alhamis. A cewar kungiyar a fadin duniya an samu raguwar wannan adadi da kaso hudu cikin dari idan aka kwatanta da shekarar 2016 inda aka samu kisan mutane 1,032 a bara kuma 993.

Kasar Guinea ta haramta hukuncin kisa ga duk wani laifi yayin da Kenya ta tashi daga tsarin nan na dole a aiwatar da hukuncin kisa ga wanda ya kashe wani. Burkina Faso ma ta samu yabon na Amnesty International bisa kudirin dokarta da ya hadar da kokari na kawar da hukuncin kisa, ita kuwa  Chadi ta takaita irin wannan hukunci ga wadanda aka kama da laifi na ta'addanci. A cewar Salil Shetty sakatare janar na kungiyar ta Amnesty International wannan mataki da aka gani a kasashen na Afirka kudu da hamadar Sahara abu ne da ke kara karfin gwiwa.