Hukuncin daurin rai da rai ga Morsi | Labarai | DW | 18.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukuncin daurin rai da rai ga Morsi

Kotu a Masar ta yankewa tsohon shugaban kasar Muhammad Morsi daurin rai da rai bayan da ta ce ta same shi da hannu kan laifi na cin amanar kasa.

Kotun ta daure Morsi din ne da wasu mutane bayan da ta ce an same su da laifi na yi wa daular Qatar leken asiri. Baya ga wannan laifi, kotun har wa yau ta sami Morsi din da laifi na agazawa wasu kungiyoyi na kasashen ketare wajen taimakawa wasu tserewa daga gidan kaso. Kotun ta kuma yankewa mutum shidda wadanda 'yan kungiyar nan ce ta 'yan uwa Musulmi kana na hannun daman Morsi hukuncin kisa saboda laifi na cin amanar kasa. Kotun dai ta bawa Morsi din damar daukaka kara idan bai gamsu da wannan hukuncin da aka yanke masa ba.