Hukuncin daurin rai da rai a Masar | Labarai | DW | 04.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukuncin daurin rai da rai a Masar

Masufafutuka 230 da suka jagoranci juyin-juya halin da yayi awon gaba da gwamnatin tsohon shugaban kasar Masar Hosni Mubarak a 2011 za su fuskanci hukuncin daurin rai da rai.

Daga cikin wadanda wannan hukunci ya shafa dai har da wanda ya jagoranci gangamin adawa da gwamnatin ta Mubarak Ahmed Douma. Wani jami'in gwamnatin kasar ta Masar ne ya tabbatar da yanke wannan hukunci inda ya ce an kuma yankewa wasu 39 da aka samu da kanan laifuka hukuncin daurin shekaru 10 a gidan kaso kowannen su. Hukuncin wanda za a iya daukaka kara a kansa, na zaman mafi tsauri da kotun ta yanke a kan masu fafutukar da ba na kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Masar din ba. Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnatin jagoran juyin mulkin kasar da a yanzu ya dare kan karagar mulki bayan gudanar da zabe Abdel Fattah al-Sisi ke tsaka da murkushe 'yan adawa.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu