Hukuncin dauri wa ′yan Al Jazeera | Labarai | DW | 29.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukuncin dauri wa 'yan Al Jazeera

Da ma 'yan jaridan 3, sun dade hannun hukumomin Masar kafin a sami belinsu, za su yi shekaru 3 a gidan kaso bisa zargin ba da bayyanan da ba tushe.

Kasashen yamma da dama ne ke yin Allah wadai da hukuncin da wata Kotu a Masar ta yanke wa wasu 'yan jaridan gidan talbijin din Al jazeera, wadanda aka dade ana godo da su da su sako su, kafin suka amince su bayar da beli.

Kasar Canada ta ce tana takaicin wannan hukunci da aka yanke wa dan jaridar kasarta wanda ke aiki wa Al jazeerar wanda ma har ta bukaci da a maido shi gida. Mohammaed Fahmy da dan asalin Masar Baher Mohammed, wanda suke aiki tare, sun sami hukuncin dauri na shekaru uku bisa zarginsu da yada labaran da basu da tushe. Sai kuma Peter Greste, dan asalin Australiyan da aka yankewa hukunci ba tare da ya kasance a shari'ar ba.