Hukunci kotu a kan Berlusconi | Labarai | DW | 02.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukunci kotu a kan Berlusconi

Tsohon fira ministan Italiya Silvio Berlusconi ya mayar da martani bayan da wata kotun koli ta tabbatar da hukuncin ɗauri a kansa.

Kotun ta amince da hukunci ne, bayan da ta same shi da laifin ƙin biyan kuɗaɗen haraji a cikin wata harkar ta wasu kamfanonin sadarwa da ya mallaka na Mediaset. Ga dai abin da yake faɗa dangane da hukunci.

Ya ce: ''Ban yin amfanin ba da wani tsari ba na kaucewa biyan kuɗaɗen haraji kuma ina yin alfari da taimaka wa ga haɓaka tattalin arzikin ƙasata ta hanyar zuba haraji. A kwai buƙatar mu ci gaba da yin kokowa domin ƙaddamar da sauye-sauye a cikin al'amuran shari'a. Tun da farko wata kotun ce ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru fuɗu a kan tuhumar. Haka kotun ta buƙaci kotun ɗaukaka ƙara da ta sake duba ɗaya hukunci na haramta masa riƙe wani muƙami na siyasa a tsawon shekaru biyar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi