Hukunci kan shirin gwamnatin Turkiyya na gina kantuna a filin Gezi | Labarai | DW | 04.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukunci kan shirin gwamnatin Turkiyya na gina kantuna a filin Gezi

Kotu ta dakatar da shirin gina kantuna a wurin shakatawar Gezi da ke birnin Istanbul.

English: İstanbul - Taksim Gezi Park - Mart 2013 - r5 Date 17 March 2013, 16:59:00 Source Own work Author VikiPicture

İstanbul - Taksim Gezi Park

Wata kotu a birnin Istanbul na kasar Turkiyya ta dakatar da shirin yin gine- gine a wurin shakatawar nan na Gezi da aka shafe makonni ana gudanar da zanga-zangar nuna adawa da shi. Jaridun Hurriyat da Zaman na kasar ta Turkiya sun ce kotun ta tsai da wannan shawarar ne domin samun damar yin nazarin takardar da kungiyar masu tsara gine-gine a birnin na istanbul ta bayar. A ranar Laraba ne dai aka gabatar da wannan shawara da aka tsayar tun watan Juni. Kotun ta ce wannan shiri wani mataki ne da zai sake fasalin dandalin Taksim da ke kusa da wurin shakatawar. To sai dai jaridun sun ce za a iya daukaka kara game da shawarar kotun.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu