Hukunci kan karar zaben shugaban Ghana | Labarai | DW | 29.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukunci kan karar zaben shugaban Ghana

Alkalan Kotun kolin Ghana sun zauna a Accra inda suka yi watsi da hujjojin 'yan adawa tare da yanke hukuncin cewa John Dramani Mahama ne shugaban kasa na hakika.

kotun koli kasar Ghana ta zauna inda ta yanke hukunci a kan karar zaben shugaban kas da ya gudana a watan Disamban bara. Ta nunar da cewar John Dramani Mahama ne ya lashe zaben. Babbar jam'iyyar adawa ta kasar wato NPP ce ta kabulanci sakamakon zaben bisa zargin cewa an tafka magudi a cikinsa. Shi dai wannan hukunci zai kawo karshen dambarwar siyasa da kasar da ake dangantawa da madubin demokaradiyar kasashen Afirka ke fuskanta.

Shi dai shugaba John Dramani Mahama me ci ya lashe zaben na watan Disamba da kashi 50 da digo bakwai daga cikin dari na kuri'un da aka kada. Sai dai kuma daga bisani kuma jam'iyyar adawa ta NPP ta garzaya kotu domin kalubalantar wannan sakamako bisa zargin cewa an yi aringizon kuri'u. Da ma dai ana sa ran cewa alkalan kotun guda tara za su tabbatar da halarcin shugabancin Dramani Mahama ko kuma su ba da umarnin sake gudanar da wani sabon zaben shugaban kasa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu