Hukumomi sun ga gawarwaki ′yan ci-ranin Nijar | Labarai | DW | 31.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumomi sun ga gawarwaki 'yan ci-ranin Nijar

Jami'an da ke aikin ceto sun ce sun gano gawarwakin mutane 87 wanda suka rasu a cikin hamada bayan da motarsu ta lalace lokacin da suke kan hanyarsu ta shiga Aljeriya.

default

Motar 'yan ci-rani dankare da kayansu

Masu aikin ceton dai sun ce suna kyautata zaton cewar kishirwa ce ta yi sanadiyyar ruwar mutanen wanda 7 daga cikinsu maza ne, mata 32 da kuma kananan yara 48.

Da ya ke tabbatar da wanannan batun wani jami'in bada agaji da suka yi aikin gano mutanen Almoustapha Alhacen ya ce gwarwakin mutanen sun rigaya sun rube lokacin da suka isa garesu kuma tuni suka yi musu jana'iza bisa tsarin addinin Islama.

Ofishin kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya ya ce akalla 'yan cirani dubu 30 ne tsakanin watan Maris da Agustan bana suka bi ta cikin hamadar sahara musamman ma dai ta Agadez, don ketarawa zuwa kasashen Turai da nufin samun ingantacciyar rayuwa.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu