Hukumar zaben Yuganda ta wanke manyan ′yan takara | Labarai | DW | 04.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar zaben Yuganda ta wanke manyan 'yan takara

Ana kara samun manyan 'yan takara da za su fafata da shugaban Yuganda yayin da ake shirin zaben shekara mai zuwa ta 2016.

Hukumar zaben kasar Yuganda ta wanke karin dan takara daga bangaren adawa, yayin da ake shirin zaben watan Febrairu na shekara mai zuwa ta 2016. Hukumar zaben a wannan Laraba ta amince da Kizza Besigye, bayan da jiya Talata ta amince da tsohon Firaminista Amama Mbabazi.

Besigye da Mbabazi sun zama manyan wadanda za su kalubalanci Shugaba Yoweri Museveni dan shekaru 71, wanda yake kan madafun iko tun shekarar 1986 kusan shekaru 30 da suka gabata.