Hukumar zaben Iraqi tace zata soke wasu daga cikin akawatunan zabe | Labarai | DW | 03.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar zaben Iraqi tace zata soke wasu daga cikin akawatunan zabe

Hukumar zabe ta kasar Iraqi tace zata soke kashi 0.2 cikin dari na sakamakon zaben ranar 15 ga watan disamba bisa rashin tabbas na wadannan kuriu,ta kuma sanarda sakamakon karshe nan bada jimawa ba.

Komishinan zabe Adel al Lamy yace,zasu soke kuriu dake cikin akwatunan zabe 50 zuwa 70 daga yankuna dabam dabam na kewayen kasar cikin akwatunan zabe 31,000 da ake dasu.

Yace soke wadannan akwatuna ba zai shafi sakamakon da aka rigaya aka sanar a makon daya gabata ba,inda jamiyar yan shia dake mulki ke kann gaba duk da fitowar yan sunni da dama wajen jefa kuriar bayan janyewarsu a zaben farko na watan janairu.

Yace an dakatar da sanar da zaben ne saboda baiwa kwararru na kasashen waje duba yanayin da ake ciki,bayan koke koke da yan sunni sukayi na magudin zabe inda suka nemi a sake zabe a wasu yankunan.