Hukumar Tarayyar Turai ta ja hankalin Macron | Labarai | DW | 08.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar Tarayyar Turai ta ja hankalin Macron

Shugaban hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ya yi kiran shugaban kasar Faransa mai jiran gado da ya tabbatar da daukar matakan rage barnata kudin gwamnati da zarar ya kama madafu.

A cewar Mr. Jean Claude Juncker ba kananan kudade ne ake barnatarwa ga banza ba a Faransa a yanzu.

A nata bangaren gwamnatin Jamus kuwa cewa ta yi za ta taimakawa Mr. Macron ta fuskar samarwa faransawa ayyuka.

Emmanuel Macron, shugaban Faransar na 25 ya sami nasara gagaruma a babban zaben kasar na karshen mako inda Jamus ke alkawarin hada kai da shi wajen tabbatar da daidaito a nahiyar Turai.

A cewar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel dangantakar manyan kasashen na Turai, babban ginshiki ne a tsarin alakar Jamus da kasashen ketare musamman kan batutuwan da suka shafi hulda ta amana tsakaninsu.