1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gargadi kasashen daeke makotaka da Kwango

Zulaiha Abubakar MNA
June 1, 2018

Wani sabon bincike da hukumar WHO ta gudanar ya bayyana yiwuwar kara samun kusan mutane 300 da za su kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango cikin watanni masu kamawa.

https://p.dw.com/p/2yoHZ
DR Kongo Ebola Ausbruch
Hoto: Reuters/J. R. N'Kengo

Hukumar ta WHO ta shawarci kasashen da ke makwabtaka da kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango da su dauki matakan gaggawa sakamakon yadda ake samun shige da ficen al'umma kusan dubu daya a kowace rana ta hanyoyin ruwa da jiragen sama.

Mutane 680 ne a halin yanzu suka samu rigakafin cutar a yankunan Mbandaka da Bikoro da aka fi samun yawaitar bullar cutar ta Ebola a kasar.