1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar IAEA ta goyi bayan kudurin da ya kushe shirin makamashin Nukiliyar Iran

November 18, 2011

Kasashe 15 dake kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya sun yi zargin Iran da sarrafa makamashin nukiliya kuma sun shawarci hukumar kula da makamashi na duniya IAEA ta fadada tattaunawarta da ita

https://p.dw.com/p/13DQN
Tutar hukumar IAEAHoto: AP

Hukumar kula da makamashi ta duniya wato IAEA a wannan juma'ar ta amince da wani kuduri wanda ya ke nuna damuwarta dangane da makamashin nukiliyar Iran wanda mambobin dindindin na kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya suka gabatar. Wannan kuduri ya bayyana cewa wajibi ne Iran da hukumar kula da makamashin su fadada tattaunawar su, hakanan kuma ta yi kira ga gwamnati a Tehran da ta bada hadin kai ba tare da ta bata lokaci ba wajen gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyar ta a karkashin tanadin kudurin kwamitin sulhun. Wannan matakin na zuwa ne bayan da wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya zargi Iran da sarrafa makaman kare dangi. Hukumar wadda ke da kasashe wakilai 35 ta amince da kudurin da gagarumin rinjaye bayan da kasashe 32 suka goyi bayan sa 2 suka ki amince da shi a yayin da kasa guda ta yi rowar kuri'arta.

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita: Ahmed Tijani Lawal