Hukumar binciken sararin samaniya ta tarayyar Turai ta tura wanim kumbo zuwa duniyar tauraron nan Venus. | Labarai | DW | 09.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar binciken sararin samaniya ta tarayyar Turai ta tura wanim kumbo zuwa duniyar tauraron nan Venus.

Hukumar binciken sararin samaniya ta tarayyar Turai, ta tura wani kumbonta zuwa duniyar tauraron nan Venus, wanda shi ne na biyu mafi kusa da rana a sararin samaniya. Tun da sanyin safiyar yau ne aka harba rokar da ke dauke da kumbon daga tashar `yan sama jannatin nan na Rasha da ke Baikonur a kasar Kazakhstan. Kumbon zai binciko yanayin tauraron Venus din, mai cike da hazo, da kuma dumamar yanayin, don ba da haske ga binciken da masana kimiyya ke gudanarwa a nan duniyar tamu, don gano dalilan da ke janyo dumamar namu yanayin. Kumbon dai zai yi kusan kwanaki dari da 62 ne kafin ya kai duniyar ta tauraron Venus. Zai kuma kusanci tauraron ne, har zuwa kusan kilomita dari 250. Tun shekarar 1990 ne dai aka kumbon nan na Amirka, wato Magellan ya kai ziyara a duniyar tauraron na Venus.