Huguette Tolinga matashiya mai kada ganga a Kwango | Himma dai Matasa | DW | 09.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Huguette Tolinga matashiya mai kada ganga a Kwango

Kalubalantar duniya da kade-dade: Tun tana shekara bakwai da haihuwa Huguette Tolinga ta fara kada ganga. A Kinshasa, kada ganga abu ne da aka tanadar wa maza kawai.

A kasar Kwango, wata matashiya mai shekaru 22 ta bugi kirji a koyon kade-kaden ganguna da a yanzu take karfafa guiwar sauran mata da ke kasar da su tashi tsaye don kawo sauyin al'adar da ke hana mata tabbatar da burinsu.

Huguette Tolinga matashiya 'yar shekaru 22 da haihuwa, ta kasance mai sha'awar kade-kade a rayuwarta, saboda haka nema ta dau tsawon shekaru 15 tana koyon salon kada ganguna a duk inda take.

"A duk lokacin da na tsinci kaina a kan dandamali ina kida, ji nake tamkar ba ni ba. To amma da ga karshe dai na tsinci kaina cikin harkar gadan-gadan."

Kasar Kwango dai ta haramta wa mata yin kade-kade, to amma Huguetta Tolinga na amfani da sha'awar da take da ita a fannin raye-raye don koyon salon kada gangunan da kashin kanta.

Kwalliya ta fara biyan kudin sabulu

Ta ce ta sha fama kan iyayenta su bata kwarin guiwa kan abin da ta sa gaba. A yanzu dai dangi da ma sauran maza masu kade-kade na matukar alfahari da Huguette Tolinga. Wani matashi a Kinshasa na daga cikin wadanda suka gamsu da irin sauyin da matashiyar ke tafiya a kai.

"Ina sauran ma'amala da ma sauran ayyukana da maza. To amma a gareni Huguetta macec e mai kamar maza, ganin irin fafutukar da take yi a kan abubuwan da take sha'awa."

Farfesa André Yoka wani mai bincike a cibiyar al'adun kasar Kwango, ya ce kade-kade na da muhimmanci ga rayuwar al'ummar kasar, to amma ba kasafai ake samun mata ke zagewa a harkar ba ganin yadda al'adun kasar ke taka wa mata birki.

"Mata suna da muhimmanci matuka, shi ya sa ko a fagen yaki, ko farauta ba a so ka taba mace. Saboda muhimmancinsu ga nasarar da ake bukata."

Dagewa don cimma bukata

Duk da wannan dai, Huguette Tolinga ba ta sare ba kan ganin sai ta tabbatar da mafarkinta. A don haka take karfafa guiwar sauran mata da su tashi tsaye wajen cimma muradunsu. A yanzu dai Huguette Tolinga ta zama sananniya a Kinshasa. To amma babban kalubalenta shi ne wanda zai dafa mata don bunkasa harkar kade-kaden da ta sa gaba. Amma duk da haka ta ce ba zai sa ta yi kasa a guiwa ba.

"A kwana a tashi sai na bude cibiyar al'adu da zimmar koyar da matasa."

A yanzu dai Huguette Tolinga ta kasance kallabi tsakanin matan kasar Kwango, ganin yadda tauraronta ke haskawa a duk fadin kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin