Hugo Chavez yayi tayin shiga tsakanin rikicin tawayen Colombia | Labarai | DW | 16.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hugo Chavez yayi tayin shiga tsakanin rikicin tawayen Colombia

Shugaban ƙasar Venezuela Huggo Chavez, ya buƙaci takwaran sa na Colombia, Alvaro Ulribe, ya ba shi izini domin yayi ganawar ƙeƙe da ƙeƙe da shugaban ƙungiyar tawayen FARC Manuel Marulanda.

A wani jawabi da yayi ta gidan Talbajan na ƙasa, Chavez ya nunar da cewar shugaban ƙasar France Nikolas Sarkozy, ya alƙawarata rufa masa baya, a wannan haɗuwa.

Burin da su ke buƙatar cimma, shine na samun belin pisinonin yaƙi wanda yan tawayen ke riƙe da su, mussamman Ingrid Betankurt.

To saidai a yayin da ya ke maida martani a game da wannan buƙata, shugaba Ulribe na Colombia, ya ce ba zata saɓu, ba wai bingida a ruwa.

Hukumomin Colombia, sun ƙaddamar da wani gagaramin yaƙi a kann yan tawayen, to saidai har ya zuwa yanzu, ba su cimma nasara ƙwato yankin kidancin ƙasar ba, da ke cikin hannun FARC.