Hugo Chavez ya dawo Venezuela | Labarai | DW | 18.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hugo Chavez ya dawo Venezuela

Ba zato ba tsammani, shugaban ƙasar Venezuela ya sauka birnin Caracas, bayan watani biyu da ya share a asibitin ƙurraru ta ƙasar Kuba, inda ya yi fama da rashin lafiya.

Ba zato ba tsammani, shugaban ƙasar Venezuela Hugo Chavez, ya bada sanarwar dawowa gida a birnin Caracas, bayan watani biyu da ya share a wata asibitin ƙurraru ta ƙasar Kuba, inda ya yi fama da rashin lafiya.

A sanarwar da ya rubuta cikin kafar sadarwarsa ta Twitter, Chavez ya ce godiya ta tabbata ga Allah da ya maido ni gida Venezuela, inda zan ci gaba da karɓar magani.

Sannan ya jinjinawa al'umar ƙasarsa, game da haɗin kai ,da kuma ƙaunar da su ka nuna masa.

Ranar 10 ga watan da ya gabata, ta kamata a rantsar da Hugo Chevez a wani saban wa'adin

mulki na shekaru shida, amma kotin tsarin mulkin ƙasar Venezuela ta ɗage rantsuwar, dalili da rashin lafiyar shugaban ƙasa.

Hugo Chavez mai shekaru 58 a duniya ya hau karagar mulkin Venezuela tun 1999, wato shekaru kusan 14 kenan da suka gabata.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Zainab Mohammad Abubakar