Hu Jintao ya fara ziyarar aiki a makotan kasashe | Labarai | DW | 15.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hu Jintao ya fara ziyarar aiki a makotan kasashe

Da safiyar yaune shugaban kasar Sin Hu Jintao, ya fara wata ziyarar aiki, a kasashe uku na Asia, da suka hada da Laos da India da kuma Pakistan.

Wannan ziyara an bayyana ta da cewa itace irin ta ta farko ga shugaban ,a tun lokacin daya dare mulki.

Bayanai dai sun nunar da cewa, da alama wannan ziyara tazo ne da nufin kyautata dangantakar dake akwai, a tsakanin kasar ta China da kuma makotan nata.

A lokacin ziyarar a cewar rahotanni, Hu Jintao zai kuma halarci taron kungiyyar hadin kann tattalin kasashen Pacific da kuma Asia, ciki har da Amurka.

A lokacin taron an shirya cewa Mr Hu Jintao, zai kuma yi ganawar bayan fage da shugaba Buash na Amurka da kuma faraministan Japan Shinzo Abe.