HRW: Najeriya ta gaza yin hukunci kan kisan’yan Shi‘a | BATUTUWA | DW | 12.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

HRW: Najeriya ta gaza yin hukunci kan kisan’yan Shi‘a

A wani rahoto da ta fitar kungiyar kare hakkin bil Adama ta duniya Human Right Watch ta zargi gwamnatin tarrayar Najeriya da gaza hukunta jami’an tsaron da ake zargi da kisan daruruwan ‘yan shi’a a kasar.

Tun kusan watan Disambar shekara ta 2015 ne dai alamun ta bacin ya fara baiyyana bayan wani fito na fito tsakanin rundunar sojan tarrayar Najeriya da kungiyar IMN ta mabiya darikar Shi’a a birnin Zaria. Bayan lafawar kurar dai ‘yan shi’ar sun ce an hallaka mabiyansu 347 a cikin artabun da ya faro daga takkadama bisa damar hanya ta wucewa ga shugaban sojojin kasar.

Ko bayan nan dai wasu jerin arangama a tsakanin  mabiyan kungiyar da jami’an tsaro sun kai ga asarar wasu mutanen 110 a biranen kaduna da kano da katsina  da Yobe da Plateau da kuma Abuja a wani abun dake nuna alamun lalacewar lamura a tsakanin yan shi’ar da ke fafutukar tabbatar da ‘yancin shugabansu Ibrahim El-zakzaky da kuma jami’an tsaron da ke fadin sun wuce makadi da rawa.

To sai dai kuma rahoton kungiyar Human Right Watch mai fafutukar kare hakkin bil’adama ya zargi gwamnatin da kasa hukunta jami’an tsaron da ma daukacin wadanda ake zargi da kisan gillar da kuma take hakkin ‘ya’yan kungiyar wadanda basa dauke da makamai .

Rahoton a cewar Aniete Ewang da ke zama mai bincike ta kungiyar a tarrayar Najeriya da kuma ta bi daddigin rikicin na kusan shekaru Uku, ya tabbatar da al’adar gwamnatin kasar na kau da ido ga cin zarafi kan bisa fararen hula.

Kungiyar ta ce a matsayin dimukaradiyya dole ne gwamnatin ta tabbatar da binciken duk wani zargin take hakkin bil’adama a bangaren jami’an tsaro ko dai ga batun kisan ‘yan shi’a ko kuma a yankin arewa maso gabas a rikicin Boko Haramun.

Duk da cewar gwamnatin kasar ta karbi rahoton kwamitin kwarrarun da ta kafa domin nazarin zargin take hakkin bil adama a bangaren jami’an tsaron, har yanzu babu alamar daukar mataki na hukunta wadanda suka aikata laifi.

Sauti da bidiyo akan labarin