Hosni Mubarak ya musunta kashe masu zanga-zanga | Labarai | DW | 13.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hosni Mubarak ya musunta kashe masu zanga-zanga

Tsohon shugaban ƙasar Masar wanda ya bayyana a gaban kotu ya kare kansa daga zargin da ake yi masa da ba da umarni ga jami'an tsaro wajen kashe ɗarurruwan jama'a a shekarun 2011.

Wata kotu a Masar ta ce nan gaba a ranar 27 ga watan da ke kamawa za ta bayyana hukunci da ta zartas a kan tuhumar da ake yi wa tsohon shugaban ƙasar Hosni Mubarak, da laifin ba da umarnin aikata kisa a kan masu yin borai na neman sauyi wanda ya kai ga share gwamnatinsa a shekarun 2011.

A lokacin da yake ammsa tambayoyi a wani zaman da kotun ta yi, Mubarak ya musunta zargin ba da umarnin ga wasu manyan jami'an tsaro wajen kashe masu zanga- zangar. Sannan ya ce wannan watakila ita ce bayanasa ta ƙarshe, saboda yadda ya ce rayuwarsa take kusan ƙarshe.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu