Hong Kong: Mutuwar dalibi ta haifar da rudani | Labarai | DW | 08.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hong Kong: Mutuwar dalibi ta haifar da rudani

Masu zanga-zanga a yankin Hong Kong sun nemi a yi wani zama na dirshan don jimamin mutuwar wani dalibin jami'a da ya rasa ransa a sakamakon arangama a tsakanin 'yan sanda da masu bore.

Rahotannin na cewa, dalibin ya fado kasa daga wani ginin gareji bayan da 'yan sanda suka fesa wa dandazon masu zanga-zangar barkonon tsohuwa, kafin ya mutu a wannan Juma'a a sakamakon raunin da ya samu daga faduwar.

Jim kadan da sanarwar rasuwar dalibin mai shekaru ashirin da biyu, masu zanga-zangar suka kara daura damara, inda suka nemi a gudanar da gagarumin gangami don ganin an hukunta wadanda keda hannu a mutuwar dalibin.

Fiye da watannin hudu kenan, ana zanga-zanga a yankin a game da adawa da dokar tusa masu laifi zuwa kasar Chaina da gwamnatin Hong Kong din ta kudiri niyyar yi, kafin ya rikide na son neman sauyin gwamnati.