Hong Kong: An saki madugun ′yan fafutuka | Labarai | DW | 09.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hong Kong: An saki madugun 'yan fafutuka

Hukumomi a yankin Hong Kong sun saki madugun 'yan fafutukar tabbatar da dimukradiyya na yankin Joshua Wong wanda aka tsare shi.

Kotu ce dai ta umarci da a saki Mr. Wong bayan wani takaitaccen zama da ta yi kan batun tsare shi inda ta ce bata ga hujjar kama shi da aka yi ba kamar yadda ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA.

A wani sako da ya sanya shafinsa na Facebook a kan hanyarsa ta zuwa Jamus, Joshua Wong dan shekaru 22 da haihuwa ya ce zai cigaba da fafutuka wajen ganin lamura sun sauya a yankin na Hong Kong.

Tun cikin watan Yunin wannan shekarar ce dai Wong da magoya bayansa suka fara gudanar zanga-zanga a kan titunan yankin don nuna adawarsu da gwamnatin yankin kan batutuwa da dama ciki kuwa har da daftarin dokar nan da ya tanadi mika masu laifi ga China don yi musu shari'a.