1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hong Kong na shirin yin watsi da dokar da ta janyo borai

Pfalzgraf Markus YB
June 13, 2019

Majalisar dokoki a yankin Hong Kong na Chaina ta dakatar da muhawara kan kudirin doka  mai neman izinin mika mazauna yankin Hong Kong da suka yi wa mahukuntan Chaina laifi zuwa Beijing.

https://p.dw.com/p/3KM5c
Hong Kong | Protest gegen Auslieferungen nach China & Ausschreitungen
Hoto: Getty Images/AFP/D. de la Rey

Carrie Lam babbar jami'ar gwamnati a yankin na Hong Kong ta yi Allah wadai da rikicin da ake yi inda ta nemi al'umma su gaggauta komawa tafarkin bin doka da oda. Bin doka da odar da matasan ke cewa shi ne aikinsu kamar yadda Fung Chin Ho ke cewa wani dan fafutukar kana daya daga cikin jagororin zanga-zangar. Carrie Lam dai ta ki janye kudirin dokar da ta bayyana da cewa ana bukatarta don wadanda suka aikata wa mahukutan gwamnatin tsakiya a Chaina laifi a zakulosu daga Hong Kong su fuskanci hukunci a Beijing kamar yadda shugabar gwamnatin Lam ta saba fadi a tattaunawar gidan talabijin na yankin, don haka fitowar masu zanga-zangar ba abu ne da ba ta tsammani ba. Dokar tana da cece-ku ce sai dai mataki ne da zai taimaki al'umma kamar yadda mahukuntan Hong Kong suke gani, amma dai ana ta samun masu adawa da fargaba da nuna tantama. A halin da ake ciki manyan ofisoshin gwamnati da ke a tsakiyar lardin hada-hada na Hong Kong, za su ci gaba da kasancewa a rufe har ranar Juma'a kamar yadda aka fada wa ma'aikata a wannan birni. Za a kuma rufe manyan shagunan cefane da bankuna da ke kusa da ginin majalisa, sa'ilin da a bangare guda 'yan sanda masu kayan sarki da ma wadanda ba sa sanye da kayan ke binciken ma'aikata masu zirga-zirga ko tafiye-tafiye.