Hollande na Moscow kan batun tsaro | Labarai | DW | 26.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hollande na Moscow kan batun tsaro

Shugaban kasar Faransa da a yanzu haka yake wata ziyara a Moscow don ganawa da shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi nuni da daukar matakan bai daya don tinkarar IS.

Shugaba Putin a yayin ganawar sa da Francois Hollande yace ayyukan ta'addanci ya tilastamu haduwa don tinkarar magan ce matsalar baki daya.

Kazalika a nasa bangaren Fracois Hollande, Ya bukaci kasashen Rashan da Turkiya dasu kai zuciyoyin nesa a dangane da tirka-tirkar dake a tsakanin kasashen biyu sakamakon harbo jirgin Rasha da Turkiyan tayi.

Shugabanin biyu dai na shirin daukar matakan bai daya ne domin tunkarar barazanar kungiyar IS tare da kara tsaurara matakai don samun tallafin al'umomin kasa da kasa.