Holland: Zaben ′yan majalisar dokoki | Labarai | DW | 15.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Holland: Zaben 'yan majalisar dokoki

Sama da mutane miliyan 12 da suka cancanci zabe a kasar Holland ne ke kada kuri'unsu a zaben kasar mai sarkakiya. Zaben da ake saran shugaban jam'iyyar masu kyamar baki Geert Wilders zai samu nasara.

A wannan Larabar ce ake gudanar da zaben kasa baki daya a kasar Holland, zaben da ake wa kallon ka iya sauya alkiblar siyasar nahiyar Turai.

Kasashen na Turai dai na fuskantar zabuka masu sarkakiya a wannan shekarar, inda bayan zaben kasar ta Holland, Faransa za ta biyo da zaben Shugaban kasa a cikin watannin Afrilu da Mayu, daga bisani Jamus ta gudanar da nata zaben 'yan majalisa a watan Satumba.

Shugaban Jam'iyyar masu kyamar baki watau Geert Wilders da fraiminista Mark Rutte, su ne dai ke kan gaba kamar yadda kuri'ar jin ra'ayi ta nunar.

Sai dai duk da tagomashi da jam'iyyar Wilders ke samu, wanda ake gani zai ninka kujerunta a majalisa, zai zame abu mai wuya ya samu nasarar kafa gwamnati, saboda akasarin shugabannin jam'iyyun siyasa basa muradin shiga gwamnatin hadaka tare da shi.

Jami'iyyu 25 ne dai ke fafatawar neman maye kujeru 150 na majalisar wakilan kasar.