1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hodar Iblis ta kashe mutane a Ajantina

Abdul-raheem Hassan
February 3, 2022

Jami'an kiwon lafiya na zargin an cakuda wani sinari mai hatsari ga lafiyar al'umma a hodar iblis da mutane suka shaka, an kuma umarci wadan da suka sayi sinadaran da su yi watsi da shi.

https://p.dw.com/p/46RbR
Hodar iblis
Hoto: Claudio Santisteban/ZUMA Press/imago images

Hukumomin kasar Ajentina sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 20 yayin da wasu 74 ke kwance a asibiti, bayan shakar hodar iblis da wani sinadarin guba. Rahotonnin likitoci na farko na cewa mamatan sun wahala da bugun zuciya gabannin ajalinsu bayan da suka shaki hodar iblis.

Jami'ai sun ce suna nan suna aiki cikin gaggawa don gano sinadaran da aka hada a cikin hodar iblis mai hatsari wanda ya yi ajalin mutane masu yawa, sun kuma gargadi wadanda suka sayi sinadaran da hodar iblin din a cikin sa'o'i 24 da suka wuce da su yi watsi da shi.