Hobbasar kasashen Afirka na yaki da Ebola | Siyasa | DW | 14.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hobbasar kasashen Afirka na yaki da Ebola

Kasashen duniya na iya kokarinsu na bayar da tallafi na kayayyaki da kudi dan yakar cutar Ebola amma su ma kasashen Afirka wadanda wasu ke fiskantar barazanar kamuwa da cutar su ma sun zabura dan neman mafita.

Kasashen Afirka, wadanda ke fama da cutar Ebola, da ma wadanda a halin yanzu wannan cuta ba ta kai gare su ba, sun dukufa wajen yaki da ita, ta hanyar takaita yaduwarta, da kuma fadakar da al'umma kan hanyoyin da suka dace, tare da daukan matakan rigakafi a kan iyakoki, yayin da su kuma kasashen duniya suka sanar da aniyar su ta kara tallafi kan yaki da cutar.

Bayan fadakarwa ga al'umma dai, kasashe da dama na ci gaba da daukan matakan rufe iyakokin su, tare da soke wasu mahimman shirye-shirye da dama a cikin kasashen nasu.

A kan yaki da wannan cuta ne ma, kasashe kamar su Botswana, suka bayar da tallafi na agaji da ma na kudade, dan baiwa Kungiyar Tarayyar Afirka damar taimakawa kashashen da suke fama da wannan cuta. Dr Mustafa Kalolo shi ne mai kula da harkokin agaji a kungiyar Tarayyar Afirka yana mai cewa...

« Gaskiya ne muna da matsalar yaduwar cutar Ebola a kasashe da dama, amma kuma mun kuduri aniya ta zuwa gaba tare da cin nasara, domin hakan yana da babban mahimmanci. Muna ci gaba da yin iya kokarin mu tare da ban hannun hukumar Lafiya ta Duniya OMS da ma sauran masu sa hannu cikin wannan lamari dan ganin bayan wannan annoba. »

Kafin dai a kai ga shawo kan wannan cuta ta Ebola, ana iya cewa akwai wani dan kankanen kwarin gwiwa da ake da shi dangane da maganin wannan cuta, musamman ma dangane da umarnin da hukumar lafiya da duniya WHO ko OMS ta bayar na a yi amfani da wasu magungunnan da ake sa ran zasu iya warkas da cutar, duk da cewa har yanzu maganin na a mataki na gwaji ne, wanda ake ganin idan ta tabbata, to za'a samu, a ceto rayuka da dama na al'ummar da ke fama da wannan cuta, duk kuwa da cewa akwai shakku mai yawa kan maganin.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Pinado Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin