1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hizbollah,sun cafke sojin Izraela biyu

July 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6D

Kungiyar Hizbollah dake kasar Lebanontace ashirye take ta tattauna batun musayan Prisononi da Izraela ,a dangane da sojin izraelan biyu da sojojin yakin sunkuru suka sace a yau,inji majiyar manyan jamian siyasa na kasar.

To sai dai kakakin kungiyar ta Hizbollah yaki cewa komai kann wannan batu,,inda yace cikin kwanaki masu gabatowa shugaban kungiyar shiekh Hassan Nasrallah,zai sanar da matsayin kungiyar akan prisononin.

To sai dai kasashen duniya nacigaba da Allah wadan hare haren da sojojin sa kai na hizbullah na Lebanon din suka kai a arewacin Izraela.maaikatar harkokin wajen Britania tace wannan yanayi zai iya ruruta karuwar rikice rikice a yankin baki daya.Ita kasar faransa bayyana damuwanta tayi da wannan yanayi da ake ciki ,sakamakon cafke sojojin Izraelan guda biyu,da yan hizbulla sukayi.Ita kuwa kungiyar gamayyar turai EU kira tayi dangane da sakin sojojin biyu cikin gaggawa domin kawo zaman lafiya.