Matashin jihar Adamawa mai yin alli
April 1, 2020Wannan matashi mai shekara 34 a duniya, ya rungumi sana'ar yin allin wato chalk da Turancin Ingilishi. Matashin mai suna Sugabsen Martins ya fara sana'ar ne bayan kammala karatunsa domin dogaro da kansa ta yadda ba sai ya yi aikin gwamnati ba. Ko da yake matashin ya ce ya cimma nasarori sosai da wannan sana'ar, sai dai ya ce yana fuskantar kalubale musamman ma na tsadar kayan aiki, ganin cewa daga kasashen ketare ake shigo da su da kuma matsalar wadataccen wajen yin sana'ar.
Wannan sana'ar dai ba shi kadai ke amfana da ita ba, a cewar guda daga cikin matasan da ke koyon sana'ar a gurinsa mai suna Wycliff Adama al'umma ma na cin moriyarta. Masana na ganin cewa indai har matasa zasu rungumi sana'o'in hannu, za a samu raguwar matasa marasa aikin yi. Shi ma a na shi bangaren, matashi Sugabsen Martins ya bukaci matasa da su tashi su rungumi sana'o'in dogaro da kai ba sai sun jira gwamnati ko wani nasu ya tsaya musu ba.