1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi mara hannu na sana'ar waka

July 9, 2019

Wani matashi me larurar nakasa a jihar Katsinan Najeriya da ya kammala karatunsa na NCE babu aikin yi, ya kama sana'ar yin wakoki dan dogaro da kansa.

https://p.dw.com/p/3Lp1B
Symbolbild E-Piano
Hoto: Fotolia

Matashin mai suna Abubakar tsoho ya kasance mai hannu guda, amma maimakon ya lankwashe kafufuwa ya kama bara sai ya nemarma kansa mafita kamar yadda ya shaidawa DW. Matashin ya ce a dalilin sana'ar wakar ya samu nasarori da dama wanda hakan ya kara masa azamar rike sana'ar  wakar.

Baya ga kansa da ya samarwa aiki da matashin ya yi, yanzu haka akwai wasu matasa maza da mata da ke samun na sawa a bakunanasu a karkashinsa.