1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Matashi mai horas da guragu fasahar kere-kere

March 30, 2023

Yadda wani matashi mai bukata ta musanman ya raja'a a koyar da guragu fasahar kere-keren ababen hawa domin rage musu wahalhalun sufuri.

https://p.dw.com/p/4PT0z
Wani mai bukata ta musanman
Wani mai bukata ta musanmanHoto: Moses Appiah

Wani matashi da ke Jihar Kadunan Najeriya da ya samu horo kan kere-keren kekunan guragu, bayan kammala karatunsa a makaranta ta masu bukata ta musanman da aka fi sani da School of disabled children, ya koma horar da matasa guragu sana'ar kere-keren kekunan na guragu da baburan hawa, domin saukaka wa matasa guragu wahalhalun sufuri.