1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Matashiya mai dinkin kayan kanti a Kano

February 9, 2022

Matashiya Malama Salama Usman Sadiq Maidu ta bar aikin jinyar marasa lafiya a asibiti, tare da rungumar sana'ar dinkunan tufafi 'yan kanti da koyar da su domin dogaro da kai.

https://p.dw.com/p/46l9y
Dinkin kaya 'yan kanti
Sana'ar dinka kaya 'yan kantiHoto: David Herraez Calzada/Zoonar /picture alliance

Tun bayan faduwar darajar Naira 'yan kasuwa ba sa iya shigo da irin wadannan kayayyakin, saboda tsananin tsadar su. Salama Usman Maidu dai, na dinka sutura 'yan kanti na manya da yara wadanda a baya sai daga ketare ake iya samun su. Salama dai ta ce ta taso da sha'awar dinki tun kuruciyarta, sai dai ba ta kama sana'ar ba har sai ta dalilin sabanin da ta samu da telanta kan kudin dinki sabanin da ta ce ya zama alheri a gareta. Ta nunar da cewa ta kama sana'ar dinkin gadan-gadan ba tare da ta koya ba, inda a yanzu Salama ta kware har ma tana koyawa matasa mata masu sha'awar dinkuna 'yan kantin. Sai dai duk da nasarorin da ta samu, ta ce babban kalubale a wajenta bai wuce guje mata da hakkokinta na horarwa da wasu 'yan mata ke yi kafin ta kai ga yaye su ba baya ga rashin hanyoyin tallata hajarta duk da kwarewarta.