Hillary:ta samu nasara a zaben fida gwani | Labarai | DW | 08.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hillary:ta samu nasara a zaben fida gwani

Hillariy Clinton ta samu nasara a zaɓen fida gwani wanda zai ba ta damar tsayawa takara a zaɓen shugaban Ƙasar Amirka a ƙarƙashin tutar jam'iyyar Democrat.

Shugaban Barack Obama na Amirka ya jinjina wa 'yar takara jam'iyyar ta Democrat Hillary Clinton, sakamon nasara da ta samu na samun ƙuri'un da suka cancanta domin tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa a ƙarƙashin tutar jam'iyyar Democrat.Sannan kuma ya yabawa dukkanin 'yan takarar Hillary da Bernie Sanders biyu dangane da yadda suka gudanar da yaƙin nemam zaɓen cikin nitsuwa dakuma lumana.

A yau an shirya shugaba Obama zai gana da Bernie Sanders domin tattauna a kan batun zaɓen.Da take yin jawabi a gaban dubban magoya bayanta a Brooklyn Hillary ta ayyana kanta a matsayin 'yar takarar tarhi ta jam'iyyar ta Democrat.