1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi mai saka zana a Najeriya

July 6, 2021

Wani matashi bayan kammala karatunsa ya rungumi sana'ar saka zana, inda ya shahara a jihar Adamawa da ke Najeriya.

https://p.dw.com/p/3w7j3
Niger Hungerkrise
A kan yi amfani da zana wajen rufin daki ko kuma yin rumbun adana kayan abinciHoto: AP

A cewar wannan matashin mai suna Samson Yukubu ya zabi ya nemi sana'a da zai dogara da ita, maimakon ya je ya yi maula ko fafutukar neman aikin gwamnati. Ya bayyana cewa ya samu nasarori a wannan sana'ar wace ke biya masa bukatunsa har da na wasu, kuma yana koyar da mutane sana'ar. Sai dai duk da wadannan nasarori da ya samu, Samson ya bayyna cewa ba a rasa kalubale cikin sana'ar tasa.